DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Majalisar Dokokin jihar Bauchi ta tantance sabbin kwamishinoni da gwamnan jihar ya tura ta allon gani gaka wato “Zoom”

-

 

Shugaban majalisar Dokokin jihar Bauchi

A wani ci gaban fasaha, majalisar dokokin jihar Bauchi ta kafa tarihi inda ta tantance mutum na farko da gwamnan jihar ya tura da sunan sa a matsayin kwamishina Usman Usman Shehu, ta na’urar Internet na Video wato Zoom.

Google search engine

Wannan ya nuna kudurin majalisar dokokin jihar na rungumar sabon tsari a cikin al’amuran ta, da tabbatar da rungumar fasahar zamani cikin ayyukanta.

Usman Usman Shehu, wanda dan karamar hukumar Giade ne ta jihar Bauchi, ya fara karatunsa na farko da karatun Islamiyya kafin ya wuce makarantar firamare da sakandare a jihar. Ya ci gaba da neman ilimi har zuwa jami’a a yanzu yana zaune a kasar Jamus.

Duk da anyi tantancewar ta hanyar Zoom a majalisar amma ba a samu wata matsala, inda membobin majalisar suka yi tambayoyi masu muhimmanci tare da samun ingantacciyar amsa daga Usman Usman Shehu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Hukumar tace fina-finai ta Kano ta soke lasisin wani gidan gala bisa dalilai na tsaro

Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta soke lasisin gudanar da ayyukan wani gidan gala mai suna Sunsiro Entertainment, wanda ke kan titin Yahaya Gusau,...

Dimukuradiyyar Nijeriya na cikin barazana a mulkin Tinubu – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan karancin fitowar masu kada kuri'a a zaben da aka gudanar ranar Asabar a Abuja. Cikin wani...

Mafi Shahara