DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Tinubu ya umurci jami’an soji da su ci gaba da neman ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda domin ci gaba da kakkabesu

-

 

Shugaba Tinubu

Google search engine

A cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban Nijeriya shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar  Shugaba Tinubu ya jajanta wa sojin kasar sakamakon rashin wasu jajirtattun sojoji guda shida a wani harin ta’addanci da aka kai a ranar 4 ga watan Janairu a wani sansanin sojoji na Sabon Gida a Damboa dake jihar Borno. 

Shugaba Tinubu ya yi kira da ayi cikakken bincike don gano abubuwan da suka haifar da faruwar lamarin don kaucewa  faruwar makamancin harin a gaba.

Sanarwar ta ce Shugaban ya yabawa rundunar sojin bisa martanin da suka mayar musamman bangaren jiragen sama wajen kaddamar da harin da ya yi sanadin halaka ‘yan ta’adda da dama tare da lalata dukiyoyinsu lokacin da sukai yunkurin guduwa.

Sai dai shugaba Tinubu ya bukaci sojoji da kada harin da aka kai musu ya sanyaya musu gwiwa,inda ya umarce su da su ci gaba da farautar ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda musamman yankin Arewa maso Yamma, har zuwa sansanonin su domin ci gaba da kakkabesu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin Kwale – kwale a Yobe ya karu zuwa 29

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya faru a karamar hukumar Nguru ta jihar Yobe ya ƙaru daga 25 zuwa 29,...

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa za ta tsunduma sabon yajin aiki

Kungiyar Likitocin masu neman kwarewa NARD ta bayyana cewa za ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga Litinin, 12 ga Janairu, 2026, sakamakon...

Mafi Shahara