DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rundunar sojin Nijeriya ta umurci sojojin da ke karkashin Operation Fansan Yamma da su kawar da ‘yan kungiyar ta Lakurawa ko kuma su tabbatar da korarsu daga yankunan kasar

-

CDS Christopher Musa

 

Kwamandan rundunar hadin gwiwa da ke kula da yankin Arewa maso yamma, Operation Fansan Yamma’ Maj, Gen. Oluyinka Soleye ya bayar da wannan umurni ne a ranar Juma’a a lokacin da ya kai ziyara ga sojojin da ke Balle, karamar hukumar Gudu ta jihar Sakkwato.

Google search engine

Da yake jawabi ga sojojin, Soleye ya yi kira da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu, tare da ba su tabbacin samun cikakken goyon bayan hedkwatar rundunar.

Ya kuma umurce su da su yi duk abin da za su iya don kawar da kungiyar ta Lakurawa ko kuma su tabbatar da koras su gaba daya daga yankin.

Sai dai Soleye ya yaba wa sojojin bisa jajircewarsu, inda ya yi alkawarin bayar da goyon baya ga rundunar ta yadda za a samu nasarar aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Idan rikicin PDP ya ki ci, ya ki cinyewa za mu shiga kawance in ji Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa dole na iya sanyawa jam’iyyar ta shiga kawance da wasu jam’iyyu idan ƙoƙarin da ake...

‘Yan sandan Nijeriya sun sanar da dawo da aiwatar da dokar lasisin gilashin mota mai duhu

Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta sanar da cewa za ta sake fara aiwatar da dokar lasisin gilashin mota mai duhu (Tinted Glass Permit), duk da...

Mafi Shahara