DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sojoji na bukatar kayan aiki na zamani don yakar ‘yan bindiga da masu aikata manyan laifuka – Matawalle

-

Ministan kasa a ma’aikatar tsaron Nijeriya/Bello Muhammad Matawalle

 

Ministan kasa a ma’aikatar tsaron Nijeriya, Bello Matawalle, ya bukaci a kara hada kai da samar da kudade ga bangaren tsaro domin yakar ‘yan bindiga da sauran miyagun laifuka a fadin kasar kasar.

Google search engine

Matawalle ya yi wannan roko ne a yayin kare kasafin kudin shekarar 2025 na ma’aikatar tsaro ga kwamitocin tsaro na majalisar dattawa da ta wakilai a Abuja.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar tsaro, Daberechi Asonye, ​​ ranar Alhamis a Abuja.

Ministan ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa  da ‘yan majalisar, inda ya kara da cewa duka kwamitocin majalisar da na dattawa sun nuna jajircewa da hadin kai domin tabbatar da ma’aikatar tsaro ta samu abinda take bukatawa don ganin an kori ‘yan bindiga da sauran bata gari.

Ya ce wgoyon bayan da suka ba su ya taimaka matuka wajen nasarorin da ma’aikatar ta samu zuwa yanzu. Sai dai ya ce akwai bukatar samun sabbin kayan aiki domin ci gaba da tunkarar kalubalen tsaro a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An fara shari’ar magoya bayan Senegal 18 da ake zargi da tayar da hargitsi a wasan ƙarshe na AFCON

An fara shari’ar magoya bayan Senegal 18 da ake zargi da tayar da hargitsi a lokacin wasan ƙarshe na gasar AFCON 2025 da Senegal ta...

Na yi kokarin kare ‘yan wasana ne daga zalunci a wasan karshe na AFCON – Pepe Thiaw

Kocin kasar Senegal, Pape Bouna Thiaw, ya ce zafin zuciya ne ya sa ya umarci ’yan wasansa su fice daga fili a wasan ƙarshe na...

Mafi Shahara