DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Adalcin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sa na dawo da rarar Naira miliyan 100 – Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano

-

Kwamishinan kananan hukumomi da sha’anin masarautu na jihar Kano Alhaji Tajo Usman , ya ce adalci da shugabanci na gari na gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya sa ya dawo da kudi da suka yi rara har miliyan 100.

Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Jumma’a a Kano.
Alhaji Tajo Usman, ya ce bai yi zaton gwamnan zai bayyanawa Duniyae abinda ya yi ba kasancewar yayi ne domin koyi da halaye nagari irin na gwamnan.
Kwamishinan wanda tsohon jami’in hukumar hana fasakwauri ta Najeriya wato Custom ne , ya samu sam barka tare da jawo cece kuce bayan da ya mayar da rarar naira miliyan 100, na kudaden samar da tufafin daliban firamare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara