DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Al-Hilal ba za ta yi wa Neymar Jnr rijista ba

-

Kungiyar kwallon kafa ta Al Hilal dake kasar Saudi Arabia, ba zata yi wa gwarzon dan wasan kasar Brazil Neymar Junior rijistar buga zagaye na biyu na gasar kakar wasannin firimiyar kasar ba ta 2025.

Hakan ya biyo bayan nazarin lafiyar dan wasan da tawagar ta yi na irin gudunmowar da zai bawa kungiyar.
A baya Neymar ya samu zunzurutun kudi Euro Miliyan 101 a shekarar 2024, a wasanni biyu kacal da ya shafe mintuna 42 a cikin filin wasa.
Ya shafe tsawon watanni 6, ya na fama da jinyar rauni abinda ya sa a yanzu haka Al Hilal ke dari -darin tsawaita kwantiragin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babban layin wutar lantarkin Nijeriya National Grid ya fadi

Babban layin wutar lantarki na ƙasa ya fadi Litinin din nan, lamarin da ya jefa ’yan Nijeriya da dama cikin duhu bayan da manyan tashoshin...

‘Yan bindiga sun kai hari a wani kauye na jihar Kebbi

’Yan bindiga sun kai hari a kauyen Gebbe da ke karamar hukumar Shanga a jihar Kebbi, inda rahotanni ke nuna an rasa rayuka yayin da...

Mafi Shahara