DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kananan hukumomi za su karbi kason kudinsu kai tsaye daga gwamnatin tarayya a watan Janairu – Fadar Shugaban kasa

-

Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa daga karshen watan Janairun 2025, kananan hukumomi Najeriya zasu fara karbar kason su na tarayya kai tsaye cikin asusun su.

Babban Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Mista Sunday Dare ne ya bayyana haka a wata hira ta kai tsaye da gidan Talabijin na Arise.
Dare ya ce gwamnatin shugaba Tinubu zata tabbatar da bin hukuncin kotun koli na watan Yuli 2024 da ya bai wa kananan hukumomi ikon tasarrufi da kudaden su.
Hukuncin ya biyo bayan karar da gwamnatin tarayya karkashin ministan shari’a Lateef Fagbemi ta shigar a baya kan gwamnonin jihohi, da ta bukaci ‘yancin kananan hukumomin Najeriya 774 , wajen yin amfani da kudaden su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tinubu ya fasa bai wa Abdullahi Ramat mukamin shugabancin hukumar NERC?

A wata wasika da shugaban Nijeriyar ya aike wa Majalisar Dattawa a cikin makon nan, Tinubu ya bukaci sanatoci su amince masa ya nada Aisha...

Hukumar KAROTA ta mika wa HISBAH motocin barasar da ta kama a Kano

Hukumar Kula da Harkokin sufiri ta Jihar Kano wato KAROTA ta mika manyan motoci guda uku da ke É—auke da kwalaben giya na miliyoyin naira...

Mafi Shahara