Kasar Brazil ta yi wa Nijeriya maraba da shiga cikin kawayen kungiyar kasashen BRICS da tattalin arzikinsu ke bunkasa wacce kuma ke neman zama kishiya ga kasashen Yamma.
Ministan harkokin wajen Brazil ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Jumu’a.
Nijeriya ta kasance kasa ta tara da ta kulla alaka da kasashen BRICS, baya ga kasashen Belarus, Bolivia, Cuba, Kazakhstan, Malaysia, Thailand, Uganda, da kuma Uzbekistan.