DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mahajjata daga Nijeriya za su biya Naira milyan 8.4 kudin aikin hajji a shekarar 2025

-

 

Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yada labaran hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar a ranar Litinin. 

Google search engine

Sanarwar ta ce hukumar karkashin jagorancin shugabanta Farfesa Abdullahi Sale Usman tare da manyan sakatarorinta da masu ruwa da tsaki sun cimma matsaya bisa duba na tsanaki kan kudin da kowane Alhajin Nijeriya zai biya a shekarar 2025.

A cewar sanarwar mahajjatan da suka fito daga shiyyar Borno da Adamawa,za su biya Naira miliyan 8.3.Hakazalika, maniyyatan da suka fito daga jihohin Kudu za su biya Naira miliyan 8.7.

Sai kuma alhazan da suka fito daga yankin Arewa za su biya Naira miliyan 8.4.

Shugaban hukumar Farfesa Saleh ya bukaci mahajjatan da suke son zuwa aikin Hajji da su bi dukkan ka’idojin kasar Saudiyya ta gindaya tare da jaddada muhimmancin biyan kudi da wuri da kuma yin rajista a kan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sojoji sun ceto mutane 318 da aka sace tare da kama 74 da ake zargi da hannu – Hedkwatar tsaron Nijeriya

Rundunar tsaron Nijeriya ta bayyana cewa dakarun da ke aiki a sassa daban-daban na ƙasar sun ceto mutane 318 da aka yi garkuwa da su...

Gwamnan jihar Zamfara ya gabatar da kasafin kudi N861bn na 2026 ga majalisar dokokin jihar

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da kasafin kuÉ—i na Naira biliyan 861 na shekarar 2026 a gaban majalisar dokokin Jihar a Gusau, yana...

Mafi Shahara