DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan Nijeriya milyan 70 za su amfana da tallafin kudi Naira 75,000 kowanensu don rage radadin fatara

-

Shugaba Bola Tinubu

 

Gwamnatin Nijeriya ta kammala shirye shiryen raba tsabar kudi Naira 75,000 ga ‘yan kasar miliyan 70 a wani yunkuri na rage radadin fatara.

Google search engine

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan harkokin al’umma, Hon. Aliyu Audu,ya bayyana cewa matakin ya dace da kudurin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na yakar talauci a fadin kasar.

Audu, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, ya bayyana cewa hakan ya tabbatar da shugaba Tinubu ya nuna kwazo a cikin watanni 19 kacal da ya yi yana mulkar kasar

Ya kara da cewa jajircewar manufofin Tinubu sun samar da sakamako mai kyau, wanda hakan yasa ake ci gaba da samun masu zuba hannun jari zuwa kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dalori ya karbi ragamar jagorancin jam’iyyar APC a hukumance

Shugaban riko na jam’iyyar APC, Ali Bukar Dalori, ya bukaci shugabanni da mambobin jam’iyyar da su zauna cikin hadin kai bayan murabus din tsohon shugaban...

An dakatar da jirgin Rano Air kan zargin matsalar inji – NCAA

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da wani jirgin Rano Air mai lamba 5N-BZY bayan fuskantar hatsarin gobara da matsalar...

Mafi Shahara