DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan bindiga sun yi ajalin ‘yan kasuwa tare da raunata mutum 11 a Fika a jihar Yobe

-

 

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni
Yan bindigar ana  zargin sun kai farmaki kasuwar da ke ci duk sati a Ngalda karamar hukumar Fika da misalin karfe 6 na yammacin ranar Litinin da suka yi  harbe harbe tare da  fasa shaguna a kasuwar.
Wani dan karamar hukumar Fika Dauda Yakubu Damazai, ya shaida wa Daily Trust cewa wasu ‘yan kasuwa guda bakwai a babbar kasuwar shanun sun rasa rayukansu a wannan mummunan hari.
Ya ce da yammacin ranar wasu da ba a san ko su waye ba sun kai hari a kasuwar shanu da babbar kasuwar inda suka  kashe mutane bakwai tare da jikkata mutane 11, kuma tuni aka  garzaya da su babban asibitin Fika domin duba lafiyar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Wata mata ta gurfana gaban kotu a Kano bayan da aka zarge ta da auren maza biyu lokaci daya

An gurfanar da wata mata a gaban Kotun shari’ar musulunci da ke Post Office a cikin birnin Kano bisa zargin auren maza biyu a lokaci...

Ana zargin wani matashi ya yi ajalin mahaifinsa a Jigawa

Rundunar 'yan sanda ta kama wani matashi dan shekara 20 mai suna Muhammad Salisu da ake zargin ya yi ajalin mahaifinsa Salisu Abubakar inda ya...

Mafi Shahara