DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Za a gina kwalejin kimiyya da fasaha “Polytechnic” mai sunan Shugaba Tinubu a Abuja

-

 

Shugaba Tinubu

Google search engine

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya amince da a gina kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya a Gwarinpa, Abuja babban birnin kasar.

Wakilin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, an sanya wa sabuwar makarantar sunan shugaba Bola Ahmed Tinubu. 

A wata wasika mai dauke da kwanan watan 16 ga watan Junairu 2025 da aka tura ga ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya ce gwamnatin tarayya ta amince da kafa Bola Ahmed Tinubu Polytechnic,a Gwarinpa domin bunkasa fasahar zamani, kere-kere, sana’a da kasuwanci a fadin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sanata Ndume ya bukaci bincike da dakatar da dokokin haraji saboda zargin sauyin da ke ciki

Sanata Ali Ndume ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dakatar da aiwatar da sabbin dokokin sauya haraji da aka tsara fara aiki a watan...

Mawaki Davido ya koma jam’iyyar Accord Party, inda kawunsa Gwamnan Osun Adeleke ya koma

Mawaki Davido, ya sanar da shirin sa na shiga jam’iyyar Accord, inda zai bi sawun kawunsa, Gwamna Ademola Adeleke na Osun. Mawakin ya ce zai kasance...

Mafi Shahara