DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Likitoci a Abuja sun tsunduma yajin aiki sakamakon rashin biyansu albashin watanni 7

-

 

Likitoci

Google search engine

Likitocin birnin taraiya Abuja sun tsunduma yajin aiki a ranar Larabar nan sakamakon rashin biyansu albashin watanni 7 na aikin da suka yi a shekarar 2023.

Wakilin Daily Trust da ya ziyarci babban asibitin Kubwa da ke Abuja ya shaida yadda wasu majinyata ke fãma saboda rashin damar ganin likita.

Sai dai wasu masu lura da asibitin sun ce yajin aikin da ake yi zai dauki tsawon kwanaki uku ne a matsayin  na gargadi, kuma akwai yuwuwar aci gaba dayi idan gwamnati ta gaza biyan bukatun  likitocin.

Ko a kwanakin baya kungiyar likitocin ta yi gargadi ga ministan babban birnin tarayyar Najeriyar Nyeson Wike bisa shiga yajin aikin kwanaki 14 a ranar 23 ga watan Disambar 2024, inda suka bukaci ya gaggauta daukar mataki tare da biyan bukatun  na su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsadar kudin haya na hana samari aure a Sokoto – Daily Trust

Mazauna Jihar Sokoto sun koka kan tashin kudin haya, suna cewa lamarin na jinkirta aure tare da jefa matasa cikin matsin tattalin arziki da barazanar...

Kotun ƙoli ta tabbatar da ikon shugaban ƙasa na ayyana dokar ta-baci

Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da ikon Shugaban Kasa na ayyana dokar ta-baci a kowace jiha domin hana tabarbarewar doka da oda. A hukuncin da ya...

Mafi Shahara