DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaban Bola Tinubu ya nada Abba Aliyu a matsayin shugaban hukumar samar da lantarki a karkara

-

Google search engine
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Abba Abubakar Aliyu a matsayin babban Manajan Darakta na Hukumar bunkasa wutar lantarki a yankunan karkara (REA).
 
Wata sanarwa da Bayo Onanuga mai taimaka wa shugaban kan yada labarai ya fitar, ta ce nadin ya fara aiki daga 23 ga watan Junairu 2025.
 
Abba Abubakar Aliyu ya rike da mukamin mukaddashin manajan daraktan hukumar tun watan Maris na 2024 har zuwa lokacin da aka nada shi.
 
A baya, ya rike mukamin shugaban sashin kula da ayyuka na shirin samar da wutar lantarki ta Najeriya
Shugaba Tinubu ya yi ammanar cewa, Abba Aliyu zai yi amfani da dimbin Ć™warewar da yake da ita  don kara kawo  cigaba a hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sojojin Nijeriya da ke Burkina Faso sun koka kan tsawaita zamansu a kasar

Jami’an Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) guda 11 da ke tsare a Burkina Faso sun koka kan tsawaita zamansu a kasar, suna mai kira...

Jerin attajiran Afirka guda 22 a shekarar 2025 -Forbes

Attajirin Najeriya, Aliko Dangote, ya sake rike matsayi na daya karo na 14 a jere da dukiyar dala biliyan 23.9, sakamakon fara aiki da matatar...

Mafi Shahara