DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Alawar yara mai sanya maye ta fara bazuwa a sassan Nijeriya in ji hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi

-

 

NDLEA

Google search engine

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, ASN Sadiq Muhammad Maigatari, ya bayyana hakan a wata hira da yayi da manema labarai a Kano, ya ce wayar da kan iyaye ya zama wajibi su duba irin alewar ake kaiwa unguwanninsu.

Ya ce an kama alewar “Choculate” amma a cikinta ana zargin an lullube ta da abubuwan da ke sanya maye.

Maigatari ya ce ana zargin ana sayar da alewa a unguwanni ga yaran da ba su sani ba, a lokacin da za su je makaranta, ya kuma bukaci iyaye da su rika lura da wasu dabi’u da ‘ya’yansu ke nunawa a unguwanni da cikin gidajen su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan bindiga sun hallaka manoma 32 a jihar Niger

Akalla manoma 32 ne aka hallaka a hare-haren da ’yan bindiga suka kai kan al’ummomin Tugan-Makeri, Konsoko da Pissa a karamar hukumar Borgu ta Jihar...

Peter Obi ya bukaci matasa da su nuna kauna da kishin Nijeriya albarkacin ranar masoya

Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya, Peter Obi, ya bukaci ’yan Nijeriya musamman matasa su yi bikin ranar masoya ta Valentine cikin nuna kishin ƙasa da...

Mafi Shahara