DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Yaro Yaro ya zama sabon mai horar da Kano Pillars bayan dakatar da Usman Abdullahi

-

 

Yaro Yaro

Google search engine

Tsohon dan wasan tawagar Super Eagles da Borussia Dortmund Ahmed Garba Yaro Yaro ya zama sabon mai horar da kungiyar Kano Pillars.

Hakan ya biyo bayan dakatar da mai horar da kungiyar Usman Abdullah da mahukuntan kungiyar ta Pillars suka yi biyo bayan rashin abun azo gani da kumgiyar ke yi a bana.

Canjaras da kungiyar ta yi da Bayelsa United ya kara harzuka magoya baya dsshugabanni na tawagar sai Masu Gida, da hakan ke biyo bayan dukan kawo wuka na ci 4-1 da ta karba a hannun Ikorodu United ta Lagos a Larabar makon da ya gabata.

A Sanarwar da kungiyar ta fitar ta bakin shugaban tawagar Alhaji Ali Nayara, Yaro Yaro wanda tsohon dan wasan kungiyar ne ta Pillars zai jagoranci kungiyar a yanzu kafin kwamitin bincike da aka kafa kan Usman Abdullah ya kammala aikin sa don samun matsaya a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar dokokin Bénin ta amince da kara wa’adin mulki zuwa shekaru 7

’Yan majalisar dokokin Benin sun amince da sabuwar dokar gyaran kundin tsarin mulki da ke tsawaita wa’adin mulkin shugaban ƙasar daga shekaru biyar zuwa bakwai. Gidan...

Na dauki matakin doka ne domin bin hakkina a PDP – Sule Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce ya kai kara kotu ne domin kare haƙƙinsa a jam’iyyar PDP, tare da jaddada cewa ba zai...

Mafi Shahara