DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kungiyar SERAP ta maka Shugaba Tinubu kotu kan zargin kin aiwatar da kwangilolin da suka kai biliyan N167bn

-

Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta kai shugaban kasa Bola Tinubu kotu kan zargin daukar mataki kan wasu ‘yan kwangila da suka karbi sama da naira biliya N167bn daga ma’aikatun gwamnati ba tare da yin aikin da aka tsara ba.
Karar wadda SERAP ta shigar a kotun tarayya dake Lagos, ta sanya ministan shari’a kuma babban lauya na kasa Lateef Fagbemi, SAN a cikin sunayen wadanda ake kara.
Wata sanarwa da mataimakin daraktan SERAP Kolawole Oluwadare ya fitar, ta nemi kotun da ta umurci Shugaba Tinubu da ministan kudi da tattalin arziki Wale Edun, su bayyyana sunayen ‘yan kwangilar ga duniya kuma su tabbatar an gurfanar da su gaban shari’a.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ba gasa muke yi da kamfanin NNPCL ba – Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa matatar man fetur dinsa ba ta yin gasa da Kamfanin man Fetur na Nijeriya, wato...

Hukumomin mulkin sojan Nijar sun kama wasu ‘yan jarida uku na Radio Sahara da ke jihar Agadez

Rahotanni daga gidan Radio Sahara Fm da ke jihar Agadez sun tabbatar da kama wasu 'yan jaridar gidan radiyon guda uku da suka hada da...

Mafi Shahara