DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jihar Zamfara ta bankado ma’akatan bogi 2,363

-

 

Google search engine
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta bankado ma’aikatan bogi 2,363 bayan aikin tantance ma’aikatan jihar da aka gudanar, tare da like hanyar zurarewar kudin gwamnati da suka kai naira miliyan 193.6 a kowane wata.
Gwamna Dauda Lawal ne ya kafa kwamitin karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar Zamfara a watan Augustan 2024 da manufar tantance ma’aikatan jihar.
Wani bayani da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman  Idris, ya ce a yayin aikin an gano kananan yara 220 da aka sanya cikin ma’aikatan jihar kuma suke karbar albashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sojoji sun ceto wani mutum da shanu a tsakanin Kano da Katsina

Sojojin rundunar haɗin gwiwa na Joint Task Force sun yi nasarar ceto wani mutum da aka sace tare da kwato wasu shanu da ‘yan bindiga...

Majalisar Dokokin Taraba ta musanta cewa Kakakinta ya raba Naira 1000 a matsayin barka da Kirsimeti

Majalisar Dokokin Jihar Taraba tare da Zing Watch Group sun musanta rahotannin da ke yawo cewa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba, John Bonzena, ya raba...

Mafi Shahara