DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar NAFDAC ta rufe shaguna 3,000, tare da kama manyan motoci 14 da jabun magunguna

-

 

NAFDAC

Google search engine

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Nijeriya NAFDAC ta rufe shaguna 3,000 a Legas tare da kwace tireloli 14 na jabun magunguna da wa’adinsu ya kare a Onitsha da wasu sauran wurare.

A sanarwar da hukumar ta fitar ta ce ta manyan motocin dakon kaya guda 14 da ke dauke da jabun magungunan ta a Legas.

Babbar daraktar hukumar ta NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ta kuma bayyana cewa jami’an tsaro sun bankado wasu manyan shaguna da ke mãƙare da jabun magunguna a Aba a karshen mako.

A cewar sanarwar, yayin da jami’an ta suka kai sumame a wani katafaren rumbun ajiyar magunguna da ke kauyen Umumeje, Osisioma Ngwa a Onitsha, inda ake dawo da magungunan da amfaninsu ya kare tare da sabunta su domin sake sayar da su, sunyi nasarar kamawa tare da rufe rubunan ajiyar irin wadannan magunguna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

FIFA ta sanya $60 a matsayin kudin tikitin kallon kofin duniya na 2026

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ƙaddamar da sabon rukuni na tikiti a dalar Amurka 60 ga kowane ɗayan wasannin 104 na Gasar Kofin...

Likitoci sun tsunduma yajin aiki a Ingila

Ƙungiyar British Medical Association (BMA) ta tabbatar da ci gaba da gudanar da yajin aiki, bayan kashi 83 cikin ɗari na mambobinta sun amince da...

Mafi Shahara