DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Saudiyya ta ba Nijeriya tallafin ton 100 na dabino

-

Dabino

 

Ofishin jakadancin Saudiyya da ke Abuja ya gudanar da wani biki a hukumance don raba tan 100 na dabino ga Nijeriya a wani bangare na ayyukan agaji da take yi duk shekara.

Google search engine

Shirin wanda cibiyar ba da agaji da jinkai ta Sarki Salman (KSrelief) ta dauki nauyin gudanarwa, na da nufin tallafawa iyalai masu karamin karfi a fadin kasar da kuma karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.

A yayin bikin, jakadan a Nijeriya Faisal bin Ibrahim, ya bayyana kwazon masarautar ta Saudiyya kan ayyukan jin kai.

Ya kuma bayyana godiyarsa ga Sarki Salman bin Abdulaziz da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa goyon bayan da suke ba wa musulmi da al’ummomin da ba a fadin duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka AFCON za ta koma duk bayan shekaru 4 – CAF

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF, ta sanar da cewa gasar cin kofin kasashen Afrika AFCON, za ta koma duk bayan shekara huÉ—u bayan...

Tinubu ya ziyarci jihar Borno domin bude ayyuka

Shugaba Tinubu, ya ziyarci Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, domin ƙaddamar da manyan ayyuka da halartar bikin auren ɗan tsohon gwamnan jihar, Sanata Ali Modu...

Mafi Shahara