DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ba Natasha kawai ba, babu macen da na taɓa yi wa maganar banza – Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio

-

 

Godswill Akphabio

Google search engine

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi masa.

Akpabio ya bayyana hakan yayin zaman majalisar a ranar Laraba, ya ce ko kadan bai taba yunkurin yin lalata da sanatan Kogi ta tsakiya ba ko wata mace ta daban.

Ya ce shi da ‘yan uwansa, mahaifiyarsu ta basu cikakkiyar tarbiyya, don haka yana girmama mata sosai.

Ya kara da cewa yanzu haka yanada ‘ya’ya mata guda hudu, don haka ba zai taba cin zarafin wata mace kuma bai taba yin haka ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Cristiano Ronaldo zai yi ritaya daga kwallon kafa nan ba da jimawa ba

Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa zai yi ritaya daga wasa nan ba da jimawa ba, yana mai...

Gwamnatin Nijeriya ta mayar ma Amurka da martani kan kalamanta ga kasar

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa gwamnatin Amurka ta yi kuskuren fahimtar hakikanin matsalolin tsaro a kasar. Ministan yada labaran Nijeriya, Mohammed Idris, ya ce gwamnatin Nijeriya...

Mafi Shahara