DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Majalisa ta yi watsi da takardar koken Sanata Natasha Akpoti kan Godswill Akpabio

-

Natasha Akpoti

Kwamitin da’a na majalisar dattawa ya yi watsi da korafin da sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta gabatar a kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da ya shafi zargin yin lalata.

Shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen, ya bayyana haka a ranar Laraba a yayin zaman bincike da kwamitin ke yi wa Natasha Akpoti-Uduaghan. 

Sanata Neda ya bayyana cewa korafin da Natasha ta gabatar bai samu karbuwa ba saboda ya sabawa doka ta 40, na dokokin zaman majalisar dattawa, wanda ya nuna cewa ba Sanata ne ya kamata ya gabatar wa majalisar dattawa takardar koke da kanshi ko da kanta ba. 

Sai dai jaridar Punch ta rawaito cewa Sanata Natasha ba ta bayyana a gaban kwamitin binciken ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dan Amurka na farko a tarihi Robert F. Prevost ya zama sabon Fafaroma

Robert Francis Prevost, dan asalin birnin Chicago a Amurka, an haife shi a ranar 14 ga Satumba, 1955, yana da shekaru 69 a yanzu. An nada...

Bill Gates zai rarraba kaso 99% na dukiyarsa ga jama’ar duniya

Attajirin nan na duniya Bill Gates, ya bayyana aniyarsa ta raba kaso 99% na dukiyar da ya mallaka da ta kai Dala bilyan 200, ga...

Mafi Shahara