DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta yanke hukuncin zaman kaso na shekaru 95 ga masu safarar kwayoyi hudu a Nijeriya

-

 Wata babbar kotun tarayya da ke Legas da Yola a jihar Adamawa ta yanke wa Shuaibu Nuhu Isa da Zidon Zurga hukuncin daurin shekaru 95 a gidan yari, bisa samun su da laifin safarar hodar iblis ta sama da Naira biliyan 4.6.

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ne suka kama Ogbuji a filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport da ke Legas a ranar Laraba 18 ga watan Satumba, 2024, a lokacin da yake kokarin sauka jirgin Ethiopian Airline daga Addis Ababa zuwa Legas, inda ya shigo da kulli 817 na hodar iblis mai nauyin kilogiram 19.40 na kimanin naira biliyan 4.

Wannan na zuwa ne watanni 16 bayan kama dan kasuwar mai shekaru 48 kuma aka yanke masa hukunci bisa laifin safarar hodar iblis.

An fara kama shi ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, da ke Abuja, ranar Laraba, 10 ga watan Mayu, 2023, bayan ya taso daga Uganda a cikin jirgin Ethiopian Airlines ET 951, da kullin hodar iblis 93 mai nauyin kilogiram 1.986.

Daga nan ne aka gurfanar da shi a gaban mai shari’a Mobolaji Olajuwon na babbar kotun tarayya da ke Abuja, kuma aka yanke masa hukunci a ranar 13 ga Yuli, 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara