DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An bindige shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Kwara

-

 

Google search engine

‘Yan bindiga sun bingige shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar Sakaina.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na daren ranar Asabar, da maharan suka harbe shi har lahira a kofar gidansa da ke Oke Ose a birnin Ilorin.

A cewar Jaridar Daily Trust ‘yan bindigar sun bar shi a nan cikin jini ba tare da sun dauki wani abu nasa ba.

Marigayin mai shekaru 32, an ce tsohon mataimaki na musamman ne ga shugaban karamar hukumar Moro kuma shugaban matasan Fulanin jihar Kwara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

DCL Hausa na Neman Ma’aikata a Kano (Full-Time)

  DCL Hausa na gayyatar ƙwararru masu jajircewa domin cike guraben aiki na cikakken lokaci (full-time) a ofishinta da ke Kano. Ana neman mutane masu kwarewa,...

Mataimakin kwamishina ya ce ga garinku nan bayan ya fadi a jihar Ebonyi

Wani Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ogbon-Inu Taiwo Popoola, ya mutu a Jihar Ebonyi yayin da yake halartar taron shugabanci a hedkwatar rundunar ‘yan sanda da...

Mafi Shahara