![]() |
Bello Turji |
Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da bukatar bayar da belin da wasu mutane hudu da ake zargi da alaka da fitaccen dan bindiga Bello Turji.
Alkalin kotun, Emeka Nwite, a cikin hukuncin da ya yanke, a ranar Juma’a ya ce babban lauyan gwamnatin tarayya, wanda shi ne mai gabatar da kara ya gabatar da kara a kan wadanda ake tuhumar cewa sakin su zai zama babbar barazana ga tsaron kasa.
Mista Nwite ya amince da hujjojin lauyan gwamnati, David Kaswe, cewa duk da cewa bayar da belin yana hannun hurumin kotu, amma dole ne a yi amfani da wannan hukunci ta hanyar shari’a da adalci.
Alkalin ya yi watsi da bukatar bayar da belin,kazalika alkalin kotun ya amince da bukatar bangaren da Mista Kaswe ya gabatar, inda ya nemi a ba su kariya yayin da ake gabatar da shari’ar.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa Mista Kaswe ya bayar da hujjar a ranar 10 ga watan Fabrairu cewa idan har aka bayar da belin wadanda ake tuhuma za su iya tserewa.
Lauyan ya gabatar da cewa akwai shaidun da ke nuna cewa wadanda ake tuhumar sun taka rawar gani a ayyukan ta’addancin da Bello Turji ya jagoranta a yankin Arewacin kasar nan.