![]() |
Nasir Idris |
Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris, ya roki a kafa sansanin soji a karamar hukumar Arewa da ke jihar domin inganta tsaro a yankin.
Nasir Idris ya yi wannan roko ne a wata hira da manema labarai jim kadan bayan ziyarar jaje da ya kai sansanin ‘yan gudun hijira da ke Kangiwa, hedikwatar karamar hukumar Arewa a ranar Laraba.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya, NAN ya rawaito cewa a ranar Lahadi 9 ga watan Maris, wasu da ake zargin ‘yan ta’addar Lakurawa ne sun kai hari tare da halaka mutane 11 tare da kona kauyuka bakwai a karamar hukumar ta Arewa.
Kauyukan sun hada da, Dogon Daji, Danmarke, Yar Goru, Tambo, Birnin Debi, Garin Nagoro da Garin Rugga, duk a karamar hukumar Arewa.
Gwamnan ya bayyana bakin cikinsa kan wannan mummunan lamarin da ya janyo hasarar rayuka tare da yin kira ga gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar kafa sansanin soji a karamar hukumar.