![]() |
Sarki Sanusi |
Kotun daukaka kara ta jingine hukuncin 10 ga watan Janairu da ya amince da halascin dokar rusa masarautu da gwamnatin Kano ta yi, dokar da ta mayar da Sarki Sunusi kan sarautar Kano.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, da suke yanke sabon hukuncin a wannan Juma’a a kotun da ta yi zamanta a Abuja, alkalai uku sun ce mai shari’a Abubakar Liman ya yanke hukuncin ne ba tare da la’akari da cewa kotunsa ba ta da hurumi ba.
Da yake karin haske kan hukuncin justice Okon Abang ya ce a yanzu kotun ba za ta je uffan ba, har sai ta ji matakin da kotun koli ta dauka.
Bayan hukuncin kotun daukaka karar na 10 a ga watan Fabrairu, gwamnatin Kano ta garzaya kotun koli da bukatar ta yi fatali da hukuncin.