DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rundunar sojin saman Nijeriya ta halaka ‘yan bindiga 20, tare da lalata maboyar su a jihar Katsina

-

 

Google search engine

Rundunar sojin saman Nijeriya ta bayyana cewa, wasu hare-hare ta sama da jami’an tsaro suka kai a jihar Katsina sun lalata maboyar ‘yan ta’adda a dajin Unguwar Goga da ke unguwar Ruwan Godiya a karamar hukumar Faskari ta jihar.

Rundunar sojin karkashin Operation Fansar Yamma ta kai harinne da sanyin safiyar ranar Alhamis, a sansanonin ‘yan bindiga guda biyu, Gero Alhaji da kuma Alhaji Riga.

A wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na rundunar sojin saman Nijeriya, Kaftin Kabiru Ali ya fitar a daren Juma’a, ta ce harin da jiragen suka kai sun yi nasarar halaka ‘yan bindiga sama da 20, tare da samun gagarumar nasara a kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ambaliyar ruwa ta dai-daita mutane 17,000 a Kaduna da Katsina – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta bayyana cewa akalla mutane 17,000 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a jihohin Kaduna da...

Atiku ya gana da shugabannin ADC a Abuja

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya yi wata ganawa da shugabannin jam'iyyar ADC na jihohin kasar.   Atiku Abubakar ya tabbatar da hakan ne cikin wata...

Mafi Shahara