Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya soke takardun mallakar fili 4,794, saboda rashin biyan kudin haya sama da shekaru 40.
A yankin Central Area da Garki I da II, Wuse I da II, Asokoro, Maitama da Guzape, masu kadarori 8,375 ne ba su biya kudin hayar ba a cikin shekaru 43 da suka wuce.
Babban mataimaki na musamman ga ministan kan harkokin yada labarai, Lere Olayinka, da daraktan kula da filaye na hukumar kula da babban birnin tarayya, Chijioke Nwankwoeze, ne suka bayyana hakan.