![]() |
Bola Ahmed Tinubu/Sim Fubara |
Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta maka shugaban kasa Bola Tinubu kotu kan dakatar da Gwamnan jihar Rivers Fubara da mataimakiyar sa na tsawon wata shida,abinda ta ce anyi shi ba bisa doka ba.
SERAP ta yi zargin cewa matakin ya saba wa tanadin tsarin mulki da kuma bata tsarin mulkin dimokradiyyar Nijeriya.
Mambobin kungiyar a jihar Rivers su uku ne suka shigar da karar wacce aka shigar gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Juma’a.
Daga cikin wadan da ake karar akwai babban lauyan gwamnati kuma Ministan shari’a, Lateef Fagbemi SAN, da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya a matsayin wadanda ake tuhuma.
A cikin wata sanarwa da mataimakin darakta kungiyar Kolawole Oluwadare ya fitar a ranar Lahadi, ta bayar da hujjar cewa matakin na dakatar da zababben gwamnan da ‘yan majalisar jihar take hakkin jama’a ne.