DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Bankin Duniya ya nuna damuwa bisa rashin ingancin alkaluman ƙididdiga a Nijeriya

-

Tambarin bankin duniya 

Bankin Duniya ya nuna damuwarsa kan yadda Nijeriya ke fitar kididdiga maras inganci, inda ya nuna cewa sauran takwarorinta kamar Mexico da Colombia da Afirka ta Kudu da kuma Brazil sun yi mata fintikau.

Bankin ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai, karkashin jagorancin Daraktan bankin mai kula da Nijeriya, Ndiame Diop, suka kai wa Ministan kasafin kudi da tsare-tsare Sanata Abubakar Bagudu a ranar Laraba.

Google search engine

A jawabinsa yayin ziyarar Mista John Mistiaen yace tsarin kididdiga na Nijeriya yayi hannun riga na sauran kasashe takwarorinta, inda ya ba da shawarar cewa zuba jarin tsakanin dala miliyan 10 zuwa dala miliyan 15 a ayyukan kididdiga na kasar duk shekara zai inganta aikin sosai tare da daidaita Nijeriya da takwarorinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Tinubu na tuhumar Stella Oduah, da cin hancin ₦5bn

Tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Saman Nijeriya, Stella Oduah, ta gurfanar a gaban kotu Abuja ranar Laraba kan zargin cin hanci da rashawa na biliyan 5 An...

Hukumar EFCC ta sake tsare Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami

Tsohon Ministan Shari’a na Nijeriya, Abubakar Malami, na tsare a hannun EFCC bayan an gayyace shi makon jiya kan wasu mu’amaloli da suka shafi dawo...

Mafi Shahara