![]() |
Alhaji Aminu Ado Bayero |
Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke hawan Sallah da aka saba yi duk shekara, kamar yadda aka tsara gudanarwa a baya.
Sarkin ya bayyana hakan ne, a cikin wani takaitaccen faifan bidiyo da ya fitar a daren Laraba, inda ya bayyana dalilan da suka sanya aka dakatar da shirin hawan Sallar.
Ta cikin faifan bidiyon, sarki Aminu, ya bayyana cewa ya bada umarnin soke hawan ne sakamakon kokarin da malaman addinin musulunci da kuma dattawa suka yi wajen ganin an samu zaman lafiya, inda ya bukaci mazauna birnin Kano da su yi amfani da lokacin bikin Sallar wajen ziyartar yan uwa da abokan arziki tare da samun damar halartar bikin Sallah.