![]() |
Tambarin bankin duniya |
Bankin Duniya ya nuna damuwarsa kan yadda Nijeriya ke fitar kididdiga maras inganci, inda ya nuna cewa sauran takwarorinta kamar Mexico da Colombia da Afirka ta Kudu da kuma Brazil sun yi mata fintikau.
Bankin ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai, karkashin jagorancin Daraktan bankin mai kula da Nijeriya, Ndiame Diop, suka kai wa Ministan kasafin kudi da tsare-tsare Sanata Abubakar Bagudu a ranar Laraba.
A jawabinsa yayin ziyarar Mista John Mistiaen yace tsarin kididdiga na Nijeriya yayi hannun riga na sauran kasashe takwarorinta, inda ya ba da shawarar cewa zuba jarin tsakanin dala miliyan 10 zuwa dala miliyan 15 a ayyukan kididdiga na kasar duk shekara zai inganta aikin sosai tare da daidaita Nijeriya da takwarorinta.