DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Bankin Duniya ya nuna damuwa bisa rashin ingancin alkaluman ƙididdiga a Nijeriya

-

Tambarin bankin duniya 

Bankin Duniya ya nuna damuwarsa kan yadda Nijeriya ke fitar kididdiga maras inganci, inda ya nuna cewa sauran takwarorinta kamar Mexico da Colombia da Afirka ta Kudu da kuma Brazil sun yi mata fintikau.

Bankin ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai, karkashin jagorancin Daraktan bankin mai kula da Nijeriya, Ndiame Diop, suka kai wa Ministan kasafin kudi da tsare-tsare Sanata Abubakar Bagudu a ranar Laraba.

Google search engine

A jawabinsa yayin ziyarar Mista John Mistiaen yace tsarin kididdiga na Nijeriya yayi hannun riga na sauran kasashe takwarorinta, inda ya ba da shawarar cewa zuba jarin tsakanin dala miliyan 10 zuwa dala miliyan 15 a ayyukan kididdiga na kasar duk shekara zai inganta aikin sosai tare da daidaita Nijeriya da takwarorinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An haramta rufe lambar mota a jihar Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta haramta yawan rufe lambar mota ba bisa ka'ida ba, lamarin da ta ce barazana ce ga tsaron jihar. Gwamnatin...

Ana mayar da ofisoshin gwamnati saniyar tatsa a Nijeriya – Sunusi Lamido

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi, ya soki yadda shugabancin siyasa a Najeriya, ke rikidewa daga hanyar ci gaba zuwa mallakar dukjya ta hanyar yaki...

Mafi Shahara