![]() |
Donald Trump |
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da sanya haraji mai tsauri kan shigo da kaya da sassan motocin da ba a kera a kasar ba, lamarin da ya sa abokan kasuwancin Amurka ke barazanar yin ramuwa.
Trump ya bayyana haka ne a yammacin ranar Laraba.
Sai dai Firaministan kasar Japan Shigeru Ishiba ya ce kamfanin Tokyo na duba yiwuwar irin matakan da zai dauka, yayin da Mark Carney na kasar Canada ya bayyana harajin da Trump din ya sa a matsayin anyi shine saboda kasarsa.