DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Barayin daji na hallaka mutanen da suka kama bayan sun karbi kudin fansa – Wasu al’umomin jihar Kaduna

-

Uba Sani

 

Al’ummar Kauru da ke Kudancin Kaduna sun koka da yadda ‘yan ta’adda ke yin garkuwa da mutanen yankin tare da hallaka su ko da kuwa an biya su kudin fansa.

Google search engine

Kungiyar ci gaban al’ummar karamar hukumar Kauru ta nuna bakin ciki da bacin rai game da harin da aka kai wa al’ummar Surubu a masarautar Kumana, inda aka halaka mutane 3 duk da an biya kudin fansa, don haka suka roki gwamnati da ta samar musu da tsaro mai inganci.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Duniya Achi, ya fitar, ta ce wannan danyen aikin na nuni ne da yadda matsalar tsaro ke kara kamari a karamar hukumarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci karin jami’an tsaro domin yaki da ‘yan bindiga a jihar Sokoto

Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci rundunar soji, ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro su yi hadin gwiwa tare da aiki domin dakile yawaitar hare-haren ’yan...

Sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa, Kaila Samaila, ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Sanata Samaila ya sanar da hakan ne cikin wata wasika da ya aike wa shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio,...

Mafi Shahara