![]() |
| Peter Obi |
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya yi watsi da rahotannin da ke alakanta shi da jam’iyyar APC, da ya ce shi ba dan jam’iyyar ba ne, kuma ba ya nufin zama mamba ciki.
Da yake mayar da martani kan wani rahoto da ke yawo a shafukan sada zumunta inda ya yi zargin cewa an ambaci sunansa a taron jam’iyyar APC na ranar Asabar, Obi ya ce yaci karo da hakan a shafukan sada zumunta dangane da taron APCn da aka ambaci sunansa,sai dai ya ce shifa ba dan jam’iyyar APC bane kuma ba zai zauna a ciki ba.




