![]() |
Farfesa Abdullahi Sale Usman |
Shugaban hukumar aikin Hajji ta Nijeriya NAHCON, Farfesa Abdullah Sale , ya bayyana bakin cikin sa kan ajalin matafiya mafarauta su 16 da aka kashe a garin Uromi na jihar Edo.
Shugaban ya mika ta’aziyyar sa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da iyalan wadan da suka rasu da al’ummar Nijeriya baki daya.
A cewar shugaban al’ummar Nijeriya ya zama wajibi su mutunta juna a matsayin ‘yan uwa daya ba tare da banbanci ba don ci gaban kasa , kana kare rayukan kowa ya zama tilas a fadin kasar.
Farfesa Saleh ya ce ya yi matukar kaduwa tare da bakin cikin abinda ya faru na matafiyan a yankin Undune Efandion dake Uromi a jihar ta Edo da ya faru ranar 27 ga Maris 2025.
Haka zalika ya yabawa shugaban kasa Tinubu , bisa umarnin da ya bayar na kama batagarin da sukayi aika – aikar.
Ya kuma yaba da kokarin jami’an tsaro na kama Mutum 14 da suka aikata ta’addancin bisa umarnin na shugaban kasa.