![]() |
CDS Christopher Musa |
Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya yi Allah wadai da kisan matafiya a jihar Edo, tare da shan allwashin hukunta wadanda suka aikata laifin.
A ranar Alhamis din da ta gabata wasu gungun batagari a garin Uromi na jihar Edo suka yi ajalin wasu matafiya-mafarauta guda 16.
Rahotanni sun bayyana cewa wadanda harin ya rutsa da su na komawa gida ne daga jihar Rivers domin kammala azumin watan Ramadan da kuma Sallar Idi tare da iyalansu a lokacin da aka kai musu harin.
Wannan lamari dai ya sha suka daga kungiyoyi daban-daban na arewacin kasar, da gwamnatocin jihohi, da kuma ‘yan majalisar dokoki.
A wata sanarwa da daraktan yada labarai rundunar ya fitar, Brig. Janar Tukur Gusau, ya ce da an sanar da hukumomin da suka dace domin tantance sunayen wadanda abin ya shafa.
Cristopher Musa ya yi tir da kira da kakkaudar murya kan kisan da aka yi wa mafarauta, a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida da ya ce tabbas wannan abu ba zai tafi a banza ba.