DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya ya yi Allah-wadai da ajalin matafiya-mafarauta da ya faru a jihar Edo

-

CDS Christopher Musa

 

Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya yi Allah wadai da kisan matafiya a jihar Edo, tare  da shan allwashin hukunta wadanda suka aikata laifin.

Google search engine

A ranar Alhamis din da ta gabata wasu gungun batagari  a garin Uromi na jihar Edo suka yi ajalin wasu matafiya-mafarauta guda 16.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda harin ya rutsa da su na komawa gida ne daga jihar Rivers domin kammala azumin watan Ramadan da kuma Sallar Idi tare da iyalansu a lokacin da aka kai musu harin.

Wannan lamari dai ya sha suka daga kungiyoyi daban-daban na arewacin kasar, da gwamnatocin jihohi, da kuma ‘yan majalisar dokoki.

A wata sanarwa da daraktan yada labarai rundunar ya fitar, Brig.  Janar Tukur Gusau, ya ce da an sanar da hukumomin da suka dace domin tantance sunayen wadanda abin ya shafa.

Cristopher Musa ya yi tir da kira da kakkaudar murya kan kisan da aka yi wa mafarauta, a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida  da ya ce tabbas wannan abu ba zai tafi a banza ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kotu za ta yanke hukunci kan belin Abubakar Malami a ranar 7 ga Janairu

Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ta sanya 7 ga Janairu domin yanke hukunci kan bukatar beli da Abubakar Malami, tsohon Antoni-Janar na Tarayya...

EFCC ta yi watsi da zargin Gwamna Bala Mohammed na tsangwamar jami’an gwamnatinsa

Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa tu'annati a Nijeriya ta yi watsi da ikirarin da Bala Mohammed, Gwamnan Jihar Bauchi, ya yi...

Mafi Shahara