DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotun sauraren kararrakin zabe ta yi watsi da ƙarar jam’iyyar AA da ke kalubalantar zaben Monday Okpebholo na APC a matsayin gwamnan jihar Edo

-

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Edo da ke Abuja ta yi watsi da karar da jam’iyyar Action Alliance da Dan takararta Adekunle Omoaje suka shigar kan zaben gwamna Monday Okpebholo da jam’iyyar APC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa. 
A hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, kotun mai alkalai uku ta yi fatali da karar, saboda rashin gamsassun hujjoji. 
Jam’iyyar AA da Omoaje sun kalubalanci nasarar Okpebholo ya samu a zaben gwamna da aka yi a ranar 21 ga Satumba, 2024, bisa zargin rashin bin dokar zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Daukacin ‘yan majalisar wakilan jihar Enugu sun koma APC

Shugaban majalisar wakilan Nijeriya Tajudeen Abbas, ne ya sanar da hakan a zaman majalisar da aka yi a Alhamis dinnan, inda ya karanta wasikun sauyin...

Muna so a ba mu damar kafa karin kananan hukumomi – Gwamnatin Bauchi

Gwamnatin jihar Bauchi ta mika bukatar neman a bata damar kirkirar sabbin kananan hukumomi 29 a jihar. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa mataimakin magatakardar Majalisar...

Mafi Shahara