DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta musanta rahotannin da ke cewa Jamhuriyar Nijar ta fice daga cikin rundunar hadin gwiwar tsaro ta kasa da kasa

-

Christopher Musa

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta musanta rahotannin da ke cewa Jamhuriyar Nijar ta fice daga cikin rundunar hadin gwiwar tsaro ta kasa da kasa, inda ta bayyana cewa irin wannan matakin zai haifar da babbar illa ga tsaro.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja Daraktan yada labarai na hedkwatar tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana cewa MNJTF na ci gaba da kasancewa cikin rundunar hadin gwiwar tsaro a yankin, kuma dole ne a yi kokarin hana kowace kasa fita daga tsarin.

Google search engine

Ya ce bayanan da ake yadawa ba gaskiya bane, amma kasashen da ke yankin Tafkin Chadi sun Samar da rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasar ne domin magance matsalolin tsaro da ke ci musu tuwo a kwarya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Nijeriya ta kubuta daga jerin kasashen da ake zargi da almundahanar kudade

Kungiyar FATF wadda ke yaki da zambar kudade a duniya ta cire Nijeriya daga cikin jerin kasashen da ta sanya wa idanu kan almundahanar kudade. Kungiyar...

Ka fito ka bayyana wa ‘yan Nijeriya hakikanin dalilin da ya sa ka canza hafsoshin tsaro – Bukatar ADC ga shugaba Tinubu

Jam’iyyar ADC ta bukaci shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya bayyana gaskiya ga ’yan Nijeriya kan ainihin dalilan da suka sa aka yi gaggawar sauya shugabannin...

Mafi Shahara