![]() |
Christopher Musa |
Hedikwatar tsaron Nijeriya ta musanta rahotannin da ke cewa Jamhuriyar Nijar ta fice daga cikin rundunar hadin gwiwar tsaro ta kasa da kasa, inda ta bayyana cewa irin wannan matakin zai haifar da babbar illa ga tsaro.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja Daraktan yada labarai na hedkwatar tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana cewa MNJTF na ci gaba da kasancewa cikin rundunar hadin gwiwar tsaro a yankin, kuma dole ne a yi kokarin hana kowace kasa fita daga tsarin.
Ya ce bayanan da ake yadawa ba gaskiya bane, amma kasashen da ke yankin Tafkin Chadi sun Samar da rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasar ne domin magance matsalolin tsaro da ke ci musu tuwo a kwarya.