![]() |
| Malam Ibrahim Shekarau |
Kungiyar League of Northern Democrats (LND) ta Malam Ibrahim Shekarau ta zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da fifita wata kabila a kan sauran kabilun Nijeriya wajen nade-naden mukamai a gwamnati.
Kungiyar a sanarwar da mai magana da yawunta Dr. Ladan Salihu ya fitar, ta buga misali da yadda rabon mukamai na baya-bayan nan da shugaban kasa ya yi a Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) ya fi bayar da fifiko ga wata kabila fiye da sauran kabilun kasar.
LND ta ce ta san da cewa dokokin Nijeriya sun amince wa shugaban kasa ya yi sauye-sauye amma ta ce wannan mataki na fifita kabilarsa a kan sauran kabilun kasar ba daidai ba ne, kuma kungiyar ba za ta goyi bayan hakan ba, domin hakan tauye adalci da ka’idojin daidaito a raba mukaman gwamnati ne karara.




