DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Abinci da karnuka ke ci ma ya fi namu tsafta – Zargin wasu fursunonin Nijeriya

-

Fursunonin da ke gidajen gyaran hali  daban-daban a fadin Nijeriya sun yi zargin cewa ba a inganta abincinsu yadda ya kamata.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya da kwamitin mai zaman kansa da ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji -Ojo ya kafa a watan Satumbar da ya gabata domin binciken zargin cin hanci da rashawa.
Yayin da kwamitin ya tabbatar da cewa fursunonin na mutuwa saboda yunwa, sai dai mukaddashin Kwanturola Janar na hukumar ya bayyana hakan a matsayin ƙage da ƙaharu, yana mai cewa babu wata kididdiga da ta tabbatar da zargin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar dattawan Nijeriya za ta tattauna da shugaba Tinubu kan kalaman Trump

Majalisar dattawan Nijeriya ta bayyana cewa za ta gana da shugaba Tinubu da bangaren zartarwa domin tattauna batun rikicin diflomasiyya da kalaman shugaban Amurka Donald...

ECOWAS ta yi watsi da zargin Trump na halaka mabiya addinin kirista a Nijeriya

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta fitar da sanarwa mai dauke da watsi kan zargin cewa hare-haren ta’addanci da ke ƙaruwa a...

Mafi Shahara