DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Nijeriya na shirin samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 8,000 nan da shekarar 2027

-

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin samar da wutar lantarki a kalla megawatt 8,000 a karshen wa’adin mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu na farko a shekarar 2027.

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a yayin taron manema labarai karo na shida a 2025 a Abuja.

Google search engine

Adelabu ya ce abin da aka sa a gaba ya tabbata, yana mai cewa tuni fannin samar da wutar lantarki ya samu ci gaba da kashi 40 cikin 100 tun bayan hawan gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu.

Ministan ya ce ya bibiyi tarihin yadda ake samar da wutar lantarki a Nijeriya, inda ya bayyana cewa an dauki kusan shekaru 40 – daga 1984 zuwa 2022 – ana samun megawatt 2,000 zuwa 4,000 amma nan da karshen wa’adin mulkinsu za a samu megawatt 8000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An yanke wa ɗan Najeriya hukuncin ɗaurin shekaru 11 a Amurka kan damfara da ta kai dala miliyan 1.3

Wata kotu a Amurka ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai zama a San Gabriel Valley, Abiola Femi Quadri, hukuncin ɗaurin shekara 11 da wata...

Natasha ta sake shan alwashin komawa majalisar dattawa a ranar Talata

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ‘yar Majalisar Dattawa daga jihar Kogi da aka dakatar, ta shigar da ƙara ga Majalisar Dattawa tana neman su girmama hukuncin Babbar...

Mafi Shahara