DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Salihu Lukman ya zargi Gwamnonin PDP da taimaka wa Tinubu a lokacin da Atiku ke kara tabbatar da hadakar jam’iyyu

-

Rikicin cikin gida na ci gaba da kunno kai a jam’iyyar adawa ta PDP, yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ci gaba da aiwatar da manufofinsa na hadakar jam’iyyu, tare da kaucewa gwamnonin PDP, wadanda a yanzu ke fuskantar zargin marawa shugaba Tinubu baya a zaben 2027.

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Arewa maso yamma Salihu Lukman, wanda ya yi magana a madadin gamayyar ‘yan adawar, ya ce kin goyon bayan da gwamnonin PDP da suka yi na nuna hadin kai a cikin abin da ya bayyana a matsayin babbar dabarar samun nasarar zabe.

Google search engine

A cewar Lukman, babu wani dan Nijeriya mai kishin tabbatar da sauyin dimokradiyya da shugabanci na gari da ya kamata ya dauki kungiyar Gwamnonin PDP da muhimmanci, ganin yadda ake zarginsu da marawa jam’iyya mai mulki baya.

Ya yi zargin ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, cewa jam’iyya mai mulki ta yi wa jam’iyyar PDP dabai bayi, ya bayar da misali da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, inda ya ce aikin Wike shi ne ke gurgunta burin jam’iyyar PDP na shugaban kasa a 2027.

Ya bayyana cewa gamayyar jam’iyyun da za su yi hadaka, na kammala tattaunawa kafin bayyana tsarinsu na ceto dimokradiyyar Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ba a take hakkin Kiristoci a Nijeriya ba – Babban hafsan tsaron Nijeriya

Babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Olufemi Oluyede ya karyata ikirarin cewa ana zaluntar Kiristoci a Nijeriya, inda ya ce babbar matsalar Nijeriya ita ce ta’addanci. Janar...

Ya kamata ka taka wa Matawalle burki – Jam’iyyar PDP ta shaida wa Tinubu

Kungiyar dattawan Arewa ta jam’iyyar PDP ta zargi ministan tsaron Nijeriya, Bello Matawalle, da jagorantar sauya shekar da dama daga PDP zuwa APC ta hanyar...

Mafi Shahara