DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sojojin Burkina Faso sun dakile yunkurin juyin mulkin a kasar

-

Gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta ce ta dakile wani yunkuri na hambarar da gwamnatin shugaban mulkin sojan kasar, Kyaftin Ibrahim Traoré, wanda suka yi zargin hannun wasu dake neman mafaka makwabciyar kasar Ivory Coast.

Ministan tsaron kasar Mahamadou Sana, ya ce tsofaffin soji da wadanda ke aiki ne suka shirya juyin mulkin, ta hanyar kai wa fadar shugaban kasa hari ne a makon jiya.

Tun shekara ta 2022 da shugaban mulkin sojan Kyaftin Ibrahim Traoré ya kwace mulki ta hanyar juyin mulki ake kokarin hambarar da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kwankwaso ba dan NNPP bane tun 2023, in ji shugaban jam’iyyar na kasa

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dr. Agbo Gilbert Major, ya bayyana cewa Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ba halastaccen da jam’iyyar ne ba. Yayin da...

Sai kun kara damara wajen yaki da matsalar tsaro – Shugaba Tinubu ya umurci sojojin Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya bukaci jami'an rundunonin tsaron Nijeriya da su kara azama wajen shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Shugaba Tinubu ya...

Mafi Shahara