DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan Afirka 18 ne ke cikin Cardinals 135 da suka cancanci yin zaben sabon Paparoma

-

  • Duk da cewa akwai manyan malaman addinin kirista wato Cardinal 252, sai dai Cardinal 135 ne kawai ke da dama kuma suka cancanci kada kuri’ar zaben Paparoma da za a yi nan gaba.

Nahiyar Turai ce ta fi kowacce yawan adadin masu zaben, inda take da Cardinal 53 da za su kada kuri’a.

Yankin Asiya, shine na biyu a yawan masu zaɓen, yayin da Nahiyar Afirka ke zama ta uku da mambobi 18 masu jefa ƙuri’ar zaben sabon Paparoma.

Google search engine

Kudancin Amurka na biye da mutum 17, yayin da Arewacin Amurka ke da masu zabe 16.

Sauran sune yankin Oceania da Amurka ta tsakiya, masu mutum hudu kowanne, sune ke da mafi karancin adadin masu zabe a babban taron da ke tafe.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Tinubu babbar kyauta ne daga Allah domin gyaran Nijeriya – Yahaya Bello

Tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana shugaban Nijeriya Bola Tinubu a matsayin babbar kyauta da Allah ya ba Nijeriya domin gyaran kasar. Yahaya Bello...

Gwamnatin Nijeriya ta ce cin jarabawar lissafi “Mathematics” wajibi ne ga daliban Sakandare kafin kammalawa

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa lallai dukkan ɗalibai masu rubuta jarabawar kammala sakandare su cigaba da rubuta lissafi tare da harshen Turanci a matsayin wajibi. Mai...

Mafi Shahara