An shiga cikin tashin hankali a birnin Yenagoa ta jihar Bayelsa, bisa karar harbe-harbe da aka ji a wurin masu biyayya ga ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike karkashin wata kungiya mai suna NEW Associates.
Kungiyar ta shirya taron ne karkashin jagorancin George Turnah, jigo a jam’iyyar PDP a jihar.
Ana ci gaba da gudanar da taron ne a lokacin da aka yi ta jin karar harbe-harbe a yankin, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.
Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan harbe-harbe, sakataren kungiyar NEW Associates a jihar Bayelsa, Comrade Ebilade Ekerefe, ya ce za su ci gaba da gudanar da taron.
A halin yanzu, magoya bayan NEW Associates sun sake haduwa don ci gaba da gangamin taron.